Kungiyar kwallon kafa ta Bayelsa United ta tabbatar da cewa har yanzu Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF bata bawa kungiyar Tukwicin Naira Milyan 25 da aka yi mata alkawari ba, bayan ta lashe gasar cin kofin Kalubale na kasa Aiteo na shekarar data gabata.
Shugaban sashin yada labarai na kungiyar, Hananeel Jackson ne ya tabbatar da haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, Yace kungiyar ta aikewa Hukumar kwallon kafa ta kasa wasikar neman basu kudaden, amma har yanzu babu wani labari.
Kazalika ya musanta wasu rahotanni dake cewa kungiyar taki mayar da Kofin Gasar, Sakamakon yadda Hukumar ta NFF taki bata kudaden.
Idan ba’a manta kungiyar ta samu nasarar lashe kofin gasar cin Kalubale ta kasa na shekarar 2021 a karon farko bayan data doke Nasarawa United a ranar 8 ga watan Augustan Bara.