Kungiyar Ma’aikatan Lantarki ta kasa tace babu wadansu kwararan nasarori da aka samu kan yarjejeniyar data kulla tsakaninta da gwamnatin taraiyya bayan shafe makwanni biyu da janyen yajin aikin data soma.
Kungiyar ta janye yajin aikin ne bayan cimma matsaya tsakaninta da gwamnati na biya mata bukatun data bijiro dasu.
Da yake karin haske kan karewar wa’adin makwanni biyu da suka bayar, jami’in kungiyar na shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan, Kwamared, Ado Riruwai, Yace duk da mabanbantan ganawar da suka yi a tsakaninsu har yanzu ba’a cimma matsaya ba.
Yace a yanzu haka suna dakon umarnin da uwar kungiyar ta kasa zata basu domin sanin mataki na gaba da zasu dauka.
Idan ba’a manta kungiyar ma’aikatan lantarki ta kasa ta shiga yajin aikin ne a sakamakon wariyar da suka ce ana nuna masu da kuma kin biyan tsaffin ma’aikatan kanfanin lantarki na kasa kamar yadda aka amince da yin haka a shekarar 2019 da sauran wadansu bukatu.