Gwamnatin tarayya ta janye sanarwar da ta yi tunda farko dangane da dawo da zirga-zirgar jiragen sama daga Hadaddiyar Daular Larabawa da Etihad Airlines a Najeriya.
Ministan sufurin jiragen sama da kula da sararin samaniya, Festus Keyamo, ya ce babu wani lokaci da aka tsayar da kamfanonin jiragen biyu za su ci gaba da zirga-zirga a Najeriya.
Wannan sanarwar ta ci karo da sanarwar farko da mai magana da yawun shugaban kasa Ajuri Ngelale ya bayar bayan ganawar da shugaba Bola Tinubu ya yi da takwaransa na daukar larabawa Sheik Mohamed bin Zayed Al Nahyan, a ranar Litinin.
Ngelale ya ce bayan ganawar kamfanin Emirates Airline zai ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Najeriya ba tare da bata lokaci ba.
Sai dai Keyamo wanda ya yi magana a taron kolin jiragen sama na Afrika da aka rufe a Abuja ranar Alhamis, ya ce ana kan kammala yarjejeniyar.