On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

HAJJIN 2023: Masu Adashin Gata Zasu Samu Kashi 40 Na Guraben Kujerun Hajjin Bana - NAHCON

Hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON ta jaddada  cewa kashi 40 na guraben aikin hajjin bana guda dubu 75 za a ware su ne ga masu biyan kudin aikin hajjin ta tsarin adashin gata.

Kashi 40 daidai yake da kujeru dubu 30.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai na NAHCON Musa Ubandawaki ya fitar.

Sanarwar ta nuna damuwarta kan yadda ake matsawa  masu biyan kudinu a karkashin shirin adashin gata na NAHCON da su yi kaura  daga tsarin zuwa hukumomin alhazai na jihar su domin a yi musu rajistar aikin hajjin bana inda aka ware kashi 60 nakujerun ga masu biyakai tsaye.

Sai dai hukumar ta  bukaci gwamnatocin jihohi da su mutunta yarjejeniyar raba kason aikin hajji ta hanyar bin ka’ida don tabbatar da adalci da samun nasarar shirin.

Har ila yau hukumar aikin hajji ta kasa  ta sake jadada ranar 28 na watan da muke ciki a matsayin rana ta karshe da zata kammala karbar kashi50 na kudaden aikin hajin bana daga hukumomin jin dadin alhazai dake sassan Najeriya.

A karshe hukumar aikin hajjin ta kasa ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkokin aikin hajjin da su cigaba da bada goyan bayansu ga hukumar domin gudanar da aikin hajjin na bana cikin nasara.