Jami’an hukumar tsaro ta DSS tare da babban bankin kasa CBN da kuma hukumar tsaro mai bada kariya ga fararen hula civil defense, sun kama wasu mutane 14 da suka hada da wata mata bisa zargin sayar da sabbin takardun naira ba bisa ka’ida ba a Kano.
Kwamandan hukumar ta civil defense na jihar Kano, Adamu Zakari shine ya bayyana haka a lokacin da yake holen wadanda ake zargin a shalkwatar hukumar ta jihar Kano da yammacin ranar Talata.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a yayin wani simame na hadin gwiwa da suka gudanar a babban birnin tarayya a wani bangare na kokarin tabbatar da matakin hana abubuwan da suka saba wa dokar CBN.
Ya ce hukumar tare da DSS da kuma CBN za su ci gaba da dakile masu aikata wannan dabi’a wanda laifi ne mai hukunci a karkashin dokar CBN, ya ce da zaran an kammala bincike kan al’amarin za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.