On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwannatin Tarayya Ta Koka Kan Halin Da 'Yan Jarida Ke Ciki Wajen Gudanar Da Aiyukansu

JARIDA

Gwamnatin tarayya ta ce ‘yan jarida a kasar nan na gudanar da aiyukan su cikin mawuyacin yanayi, wanda suka cancanci a inganta masu yanayin gudanar da aiyukansu.

Ministan yada labarai da wayar da kai  na kasa, Alhaji Mohammed Idris ne  ya baiyana haka yayin hirarsa da kanfanin dillancin labarai na kasa a Abuja.

Ya  ce  yan jarida da dama na sadaukar da rayuwarsu wajen gabatar da aiyukansu, inda  y ace  zai yi amfani da damarsa wajen ganin an inganta walwalar  yan jarida a kasar nan.

Ya kuma kara da cewar  ‘Yan jarida mallakin kasar nan ne, wanda  Najeriya  ya kamata ta yi wani abu na ciyar da likafarsu gaba, ta bangaren biyan albashi da sauran wasu abubuwa.