Gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun amince su yi aiki tare da juna domin samar da ci gaba mai dorewa da bunkasar tattalin arziki da kuma Inganta tsaro.
Gwamnonin da suka hada da na Katsina da Kano, da Zamfara da Kebbi da Jigawa da kuma Sokoto, ne suka bayyana haka bayan wani muhimmin taro da suka gudanar a gidan gwamnatin Katsina.
Yayin wani taron manema labarai na hadin guiwa jim kadan bayan kammala taron, gwamnonin sun amince da aiwatar da wata manufa guda domin tunkarar kalubalen tsaro da ya addabi yankin a shekarun baya.
Har ila yau, sun amince da yin aiki tare don inganta fannin noma, ta hanyar inganta dabaru, da samun damar shigar da kayayyakin amfanin gona zuwa kasuwannin kayayyaki.