On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnoni Sun Zargi Ministan Shari'a Da Arzuta Kansa Da Kudaden Paris Club

MALAMI DA GWAMNA KAYODE

Kungiyar gwamnonin kasar nan ta mayar da martani ga babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami SAN, bisa takaddamar wasu kudade kimanin dala miliyan 418, na kudaden Paris Club da aka dawo da su.

Da yake jawabi, kakakin kungiyar Abdulrazaque Bello-Barkindo, ya nuna takaicin sa kan shiga sharu ba shaanu da Malami ke yi kan kudaden da suka kasance  mallakin gwamnatin jihohi ne.

Idan za a iya tunawa a shekarar 2021, gwamnonin suka samu izini daga wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja, kan gwamnatin tarayya ta dakatar da dibar kudade daga asusun jihohi, kan biyan bashin kudaden Paris Club.

Bello-Barkindo, Yace Atoni janar din ya kamata yafi mayar da hankali kan yadda gwamnati zata samar da kudaden tafikas da jami’o’I da kuma harkar ilimi, ba wai samun kudaden zubawa a aljihu ba.