Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, Ya dora alhakin tada rikicin zabe da aka fuskantar a lokutan zabe na baya akan gwamnoni, inda yace sun taka muhimmiyar rawa wajen tashin zauni tsaye, ta hanyar daukar nauyin ‘yan dabar siyasa.
Oshiomhole ya baiyana haka ne a Abuja, yayin wani taro da aka shirya mai taken, Abunda zai inganta yin zabe a Najeriya, inda ya bukaci shugabannin siyasa dasu marawa yunkurin jami’an tsaro na ganin anyi zaben shekara ta 2023 cikin salama batare da samun tada jijiyar wuya ba.
Jigon jam’iyyar APCn a matakin, ya kuma yi kira da a samu hadin kai tsakanin hukumar zabe ta kasa da shugabannin siyasa da kuma hukumomin tsaro.
Tsohon gwamnan jihar Edon, Ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kokarinsa na magance kalubalen tsaro da ya addabi kasar nan.