On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Zamfara Zata Fara Aiwatar Da Sabon Albashi Mafi Kankanta Na Naira Dubu 30

GWAMNA MATAWALLE

Shugaban ma’aikatan jihar Zamfara Kabiru Gayari ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar za ta aiwatar da mafi karancin albashi na Naira dubu 30, ga ma’aikatan jihar.

Gayari ya baiyana haka ne a ranar Talata a taron wakilan kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati  ta reshen jihar  Zamfara karo na hudu a Gusau.

Shugaban ma’aikatan wanda ya samu wakilcin babban sakatare na ofishinsa  Alhaji Yusuf Bakura ya ce nan ba da jimawa ba za a shawo kan matsalar da ta kunno kai tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago dangane da batun aiwatar da mafi karancin albashi.

A saboda haka , Gayari ya yi kira ga kungiyoyin kwadagon da su kwantar da hankalinsu saboda a yanzu an kai mataki  70 cikin 100 wajen fara  gudanar da tsarin.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar kwadago ta jihar, Sani Halliru, wanda ya samu wakilcin mukaddashin sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Gusau, ya yi kira ga ma’aikata da su marawa kungiyoyin kwadago baya a kokarinsu na ganin gwamnati ta samar masu da walwala domin gabatar da aiyukansu yadda ya kamata.