
Sanata mai wakiltar mazabar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta gaji wani mummunan yanayi na tattalin arziki.
Oshiomhole ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin wata tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan ganawar sirri da mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Ya ce wasu matakai da gwamnati mai ci ta dauka su ne matakin farko na sake fasalin tattalin arziki.
A cewarsa, Tinubu da mataimakinsa sun nuna jajircewa wajen ganin an dakatar da almundahana daga gwamnatin tarayya wajen bayar da tallafi da kuma babban bankin Najeriya CBN, tare da yin kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri.