Gwamnatin tarayya ta ce, babu gudu babu ja da baya dangane da aniyarta ta kin biyan malaman jami’oin da ke yajin aiki albashinsu na watanni 5 da suka gabata, saboda kin koyar da dalibai a makarantu.
Ministan ilimi Adamu Adamu ya ce, wannan matsayi da suka dauka shi ne ya hana cimma yarjejeniyar janye yajin aikin da yanzu haka ya wuce watanni 6.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa, ministan ya ce kungiyar malaman ta ki kiran mambobinta su koma bakin aiki ne saboda kin amincewa da bukatar a biya su daukacin albashinsu na watanni 5 da suka kwashe suna yajin aikin.
Adamu ya ce bangarorin biyu sun amince tare da cimma yarjejeniya akan batutuwa da dama da aka gabatar a tattaunawar da suka yi, yayin da 4 daga cikin kungiyoyi 5 na ma’aikatan jami’oin suka amince su janye yajin da suke yi nan da mako guda mai zuwa bayan gudanar da taron shugabanninsu na kasa.
Dangane da batun biyan dalibai diyya kan hakkinsu na watanni da suka kwashe a gida suna zama lokacin yajin aikin kuwa, ministan ya ce, wannan ba hurumin gwamnati ba ne, sai da malaman da suka tafi yajin aikin.
Yace idan ‘daliban na muradin samun diyya, kada suyi kasa a gwiwa wajen yin karar kungiyar malaman jami’oi ta kasa ASUU a gaban Kotu.