Gwamnatin tarayya na shirin yin kasafin kudi na kimanin naira tiriliyan 26 da bilyan 1 a shekara mai zuwa ta 2024. Kasafin kudin ya nuna cewar an samu Karin kaso 19 da digo 15 cikin 100 na kasafin shekarar da muke ciki, wanda ya kama naira tiriliyan 21 da bilyan 83.
Ministan kasafi da tsare-tsaren cigaban kasa, Abubakar Bagudu ne ya tabbatar da haka ga wakilan kafafen yada labarai dake fadar shugaban kasa, jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwa na kasa, inda aka amince da kwarya-kwaryar daftarin kasafin kudi na shekarar 2024 zuwa 2026.
Gwamnatin tarayya na saran kasha kaso 61 da digo 63 cikin 100 na kasafin kudin shekara mai zuwa a bangaren tafiyar da harkokin ma’aikata da kuma biyan bashi.
Harkokin ma’aikata da abunda ya shafi biyan fansho zai lakuma naira tiriliyan 7 da bilyan 7 yayin da biyan basussuka zasu cinye naira tiriliyan 8 da bilyan 25, wanda jimillar kudin zasu kama naira tiriliyan 16 da bilyan 3 daga cikin gabaki dayan kasafin kudin.