Gwamnatin tarayya ta sanar da fara shirye-shiryen yashe kogin Hadeja dake jihar Jigawa a wani mataki na shawo kan ambaliyar ruwa.
Da ya ke sanar da wannan yunkuri ta cikin wani shiri na musamman a gidan Radiyon Jihar Jigawa, shugaban hukumar raya fadamun kogunan Hadeja da Jama'are wadda ke karkashin ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya, Alhaji Ma'amun Da'u Aliyu, yace matsalar ambaliyar ruwa matsala ce mai girma musamman a jihar Jigawa ko yanzu haka akwai barazana saboda mamakon ruwa da aka fuskanta a makon jiya.
"Mutane suna da wani abu da suka yi amanna da shi akan ambaliyar ruwa da yawansu suna da tunanin cewa wannan hukuma ce ke sakin ruwan kogi wanda ke kawo ambaiya, kuma a gaskiya ba haka abun yake ba masu irin wannan fahimta gaskiya fahimtarsu gurguwa ce"
"Mu muna sakin ruwa ne rani da damuna duk sanda ta kama, to kaga da haka ne za'a rika samun ambaliyar ruwa da rani"Inji Ma'amun.
(Karin Magana: ….Komai nisan gona akwai kunyar karshe)
Al’umomi a garuruwa da kauyuka masu yawa daga kimanin kananan hukumomi goma da ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Jigawa na ci gaba da kokawa tare da neman tallaffi daga gwamnati da hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu.
Mamakon ruwan sama, kamar da bakin kwarya da aka rinka samu cikin makon da ya gabata a sassan Arewacin Najeriya shi ne musabbabin ambaliyar da ta wakana a jihar ta Jigawa wadda ta lalata kayan amfanin gona da gidaje har-ma da rasa rayukan mutane a wasu Kauyuka da Garuruwa na jihar.
Yanzu haka dai gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar mutane fiye da 10 sanadiyyar wannan ambaliyar, yayin da dinbin mutane maza da mata ne suka kaura zuwa wasu garuruwa da gine-ginen gwamnati.
Sai shugaban hukumar ta raya fadamun kogunan Hadeja/Jama’are Ma’amun Da’u, yace a garin Hadeja an samu ambaliya da ta shiga gidajen mutane da yawa kuma gwamnatin jjhar tayi hobbasa domin raba al'ummarta da matsalar.
Ya yabawa gwamna Muhammad Badaru Abubakar bisa aikewa da tawaga wadda ta tattauna da hukumar kan matakan magance matsalar ambaliyar wadda gwamnatin sayo wasu na’urori irin wanda hukumar ta sayo domin yashe kogin.
Yace nan bada jimawa ba za’a hada Na’urorin domin aikin yashe kogin da nufin samun sauki daga ambaliyar ruwa.