Gwamnatin tarayya ta ce nan bada jimawa ba zata fara raba bashi ga masu kanana da matsakaitan sana’oi da kuma masana’antu a karkashin shirin bayar da tallafin naira bilyan 200 na fadar shugaban kasa.
Idan ba’a manta ba shugaban kasa, Bola Tinubu ya kaddamar da tsarin a ranar 17 ga watan Octoban bara, a wani mataki na rage radadin janye tallafin mai da kuma tsadar rayuwa da ake ciki.
Ministar Masana’antu kasuwanci da zuba jari, Doris Uzoka Anite t ace an dauki matakin ne, sakamakon nasarar aiwatar da shirin tallafawa harkokin kasuwanci mai suna NANO da ake kanyi yanzu haka.
Ta ce an warewa kowanne bangare naira bilyan 75 domin tallafawa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa ta karkashin shirin na fadar shugaban kasa, wanda kari ne akan naira bilyan 50 da ake amfani das u wajen gudanar da shirin Nano.