On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Tarayya Zata Maida Motoci Sama Da Milyan 10 Masu Amfani Da Fetir Zuwa Man Gas

CNG

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne  ya baiyana haka a yayin baje kolin mai  da iskar  gas  na shekarar  bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa  Louis Ibah  ya fitar, ya baiyaan cewar  a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu  domin  kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya  akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce  matakin wani yunkuri ne  na inganta yin amfani da Gas  a tsakanin motocin kasar  a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.