Gwamnatin tarayya ta bullo da wani tsari na inganta samar da Mamakashin iskar gas a fadin kasar nan, a wani mataki na magance matsalolin da suka shafi samar da makamashin da ake amfani das hi wajen yin girki.
Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti wanda aka dorawa alhakin bada shawarwari kan yadda za’a inganta samar da makamashin iskar gas din, da kuma karya farashinsa a cikin kasa da mako daya.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin karamin ministan Man fetir na kasa, Ekperikpe Ekpo ya fitar.
Sanarwar ta Ambato karamin ministan Mai na baiyana daukar wadan nan matakai biyo bayan tashin farashin makamashin Gas zuwa sama da naira 1 da 100 a wasu sassa na kasar nan, daga naira 700 da ake siyar dashi kan kowane Kilogiram daya.