Shugaban kwamitin sauya fasalin hanyoyin tattara haraji na kasa, Taiwo Oyedele ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewar sabbin tsare-tsaren da gwamnati ta bullo da su kan batun canjin kudin kasashen waje, za su temaka wajen inganta darajar Naira.
Ya ce tsare-tsaren wanda suka hada da yaki da duk wani haramtaccen tsarin musayar kudi zai sa darajar naira ta cike gibin da aka yi mata kafin shiga sabuwar shekarar 2024.
A yayin ganawarsa da manema Labarai a jiya, Mister Oyedele, ya ce gwamnati zata bullo da wasu dokoki a faiyace domin gudanar da canjin kudi a bisa farashi na hukuma, bayan an samar da adadin dalar da ake bukata har kimanin Dala bilyan 6 da milyan 700.