Gwamnatin Tarayya za ta horas da mata guda dubu 2, Da suka fito daga jihohin Jigawa da Adamawa da Kaduna sai nan Kano da jihar Anambra sai Neja da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, harkokin da suka shafi noma a zamanance.
Ma'aikatar kula da walwalar mata, ta ce, an tsara shirin ne domin tallafa wa kungiyoyin hadin gwiwar mata da su shiga harkar noman shinkafa domin samun riba da dorewa, tare da hadin gwiwar wata kungiyar bunkasa aikin gona a nahiyar Afrika mai suna Green Agriculture West Africa Limited wadda ta kasance reshen kamfanin China na CGC.
Ana sa ran wannan mataki na gwaji zai karfafawa mata ta hanyar kafa kungiyoyin hadin gwiwa da kuma gudanar da ayyukan noma a zamance.
Ministar Matan ta bukaci samun hadin kai da goyon baya daga masu ruwa da tsaki na gwamnati da masu zaman kansu domin kara fadada tasirin shirin.