Ministan Ma’adinai, Dele Alake ya zargi wasu manyan masu fada aji a kasar nan da hannu dumu-dumu cikin aiyukan hakar ma’adinai ta barauniyar hanya, da kuma daukar nauyin aiyukan ‘yan bindiga da ta’adanci a kasar nan.
Ministan ya yi wadannan zarge-zarge ne a yayin da ya baiyana gaban kwamitin majalisar wakilai mai saka ido kan harkokin Ma’adinai a ranar Talata, domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa.
Ya ce irin wadannan miyagun aiyuka na mutanen na temakawa wajen daukar nauyin miyagun lefuka, a maimakon su bada gudunmuwarsu wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Ya kara da cewar dole ne sai gwamnati ta yaki matsalar domin samar da cigaban da ake muradi.