Gwamnatin tarayya ta sanar da karbo wasu kudade hara naira milyan dubu 57 daga cikin naira tiriliyan 5 da bilyan 5 da hukumar tattara kudaden shiga ta kasa da sauran hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya ke bin bashi.
Babban sakatare aiyuka na musamman a ma’aikatar kudi ta kas a Okokon Ekanem Udo ne ya baiyana haka jiya a Enugu a yayin wani taron karawa juna sani, kan gano bashin da gwamnatin tarayya ke bi.
Ya ce an gano kudaden daga hannun wadanda ake bin bashi sama da mutane dubu 5 a karkashin ma’aikatun gwamnati sama da 93.
Ya ce bayanan da suke da shi sun nuna cewar mafi yawa daga cikin kanfanoni da daidaikun mutane da suka ki biyan bashin da gwamnatin ke binsu, a halin yanzu sun fara biyan bashin.