On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Tarayya Ta Gaza Magance Mafi Yawan Bukatunmu - ASUU

Kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU ta ce har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta magance yawancin batutuwan da suka sanya kungiyar ta shiga yajin aiki ba.

A karshen shekarar da ta gabata ne ASUU ta janye yajin aikinta  na watanni takwas bayan tattaunawa da gwamnatin tarayya.

Wani bangare na bukatunsu shi ne sakin kudaden farfado da jami’o’I da sake tattaunawa kan yarjejeniyar gwamnati da ASUU ta shekarar 2009, da sakin alawus-alawus na malaman jami’o’i, da amfani da manhajar UTAS wajen biyan albashi maimakon IPPIS.

Da yake magana a gidan Talabijin na Channels a daren jiya, shugaban kungiyar ASUU, Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa mambobin kungiyar; ba tare da la'akari da matsayin gwamnati ba, suna gwagwarmaya domin cimma kalandar ilimi.

Hakan na zuwa ne a lokacin da Kungiyar ta kasa ASUU ta koka kan rabon Naira biliyan 320.3 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saki domin  rabawa manyan makarantun kasarnan.

Sakataren zartarwa na Asusun Tallafawa Manyan Makarantu TETFund, Sonny Echono da  yammacin ranar Laraba ya sanar da cewa shugaban kasar ya amince da adadin kudaden na shekarar 2023 ga manyan makarantun gwamnati.

Ana saran a shekarar 2023 kowace jami’a zata karbi Naira billiyan 1.154 sai kwalejojin fasaha Naira  miliyan 699.3 yayin da kowace kwalejin ilimi za ta samu Naira miliyan 800.86.

Sai dai a wata zantawa  da gidan Talabijin na Channels a daren jiya, shugaban kungiyar ASUU, Emmanuel Osodeke, yayin da yake yabawa gwamnati kan sakin kudaden, ya bukaci a sake nazari kan tsarin rabon kudaden domin ganin kashi 90 ya tafi zuwa manyan makarantun.