Gwamnatin Tarayya na gargadin ‘yan Najeriya da ke zaune a kusa da koguna da koramu da madatsun ruwa da wuraren ambaliya, da kuma wuraren zaizayar kasa da su gaggauta kauracewa daga yankunan sakamakon tsananin ruwan sama da aka yi hasashen za a yi a watan Yuli a wasu jihohi.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa ta yi gargadin cewa jihohi 14 da garuruwa 31 za su iya fuskantar mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da zai haifar da ambaliya a cikin wannan lokaci.
Jami'in hukumar NEMA, ofishin reshen jihar Legas, Ibrahim Farinloye Farinloye, ya bukaci masu ruwa da tsaki a jihohin da abin ya shafa su dauki matakan kariya domin dakile asarar rayuka da dukiyoyi.
Garuruwan da abin ya shafa sun hada da Sumaila da Tudun Wada a Kano sai Langtang da Shendam a Jihar Filato da Shagari, Goronyo, Silame a Sokoto da Okwe, Jihar Delta da dai sauransu.