Gwamnatin tarayya tace ba ta da kudin da za ta iya biyan bukatar da kungiyar malaman Jami’o’I ASUU ta mika mata domin kawo karshen yajin aikin da suka shafe sama da wata biyu suna yi.
Karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa Festus Keyamo wanda a baya-bayan nan ya zama kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, yace hanya mafi sauki ta kawo karshen yajin aikin na ASUU shi ne Iyayen dalibai su roki kungiyar domin ganin ta baiwa yara damar komawa makarantu.
A wata zantawar Keyamo da manema labarai ranar juma’a ministan ya ce gwamnati ba za ta iya aro kudi don biyan bukatar malaman jami’ar ba, wanda ke nuna babu hanyar warware rikicin face amfani da salon shiga tsakanin Malaman da gwamnati.
Keyamo ya ce iyaye za su yi taka muhimmiyar rawa don ganin yaransu sun koma karatu ta hanyar rokon kungiyar ta ASUU.
A cewar ministan kwadagon, hatta tarukan da aka gudanar tsakanin kwamitin da gwamnati ta kafa don shiga tsakani ya gaza wajen shawo kan matsalar bayan da ma’aikatar kudi ta bada tabbacin cewa babu kudin da za a iya biyan bukatar ta ASUU.
Mr Keyamo ya ce dole ne akai ga kulla sabuwar yarjejeniya tsakanin ASUU da gwamnati don magance matsalar ta yajin aiki.