Ko kana ɗaya daga cikin waɗanda har yanzu ba a samu mitoci lantarki na zamani ba a yankinku ?, to ga wani albishir.
Hukumar kula da wutar lantarki ta kasa ta ce nan ba da dadewa ba za ta samar da mitoci miliyan hudu ga masu amfani da wutar lantarki a fadin kasarnan.
Kwamishiniyar hukumar, Aisha Mahmoud ce ta bayyana haka a wajen taron warware korafe-korafen masu amfani da lantarki da aka gudanar ranar Talata a Jos.
Mahmoud ta bayyana cewa an samar da hanyoyin samar da mitocin karkashin shirin gwamnatin tarayya samar da mitoci na kasa.
Ta ce karancin mita na daya daga cikin manyan matsalolin da hukumar ke fuskanta amma ta ce nan ba da dadewa ba zai zama tarihi.