Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya ce gwamnatin tarayya ba za ta iya ciyo bashin Naira tiriliyan 1 da milliyan 1 ba domin biyan bukatun kungiyar ASUU.
Kungiyar ta shafe fiye da wata biyar tana yajin aiki.
Umahi, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Kudu-maso-Gabas ya bayyana hakan a ranar Laraba a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga asusun tallafawa ‘yan sandan kasarnan a Abakaliki, babban birnin jihar ta Ebonyi.
Ya ce bai dace Najeriya ta ciyo bashin kudi sama da naiara trilliyan 1 domin biyan bukatar ASUU ba, duk da cewa bukatun na gaskiya ne.
Amma ya kara da cewa sannu a hankali za a iya magance bukatun.
Sai dai ya yi kira ga malaman jami’o’in da su nuna yakana da fahimta domin kawo karshen yajin aikin.
(Karin Magana: Zara bata barin dami)