Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa ta fara katse huldar dake tsakaninta da wasu kamfanonin samar da wutar lantarki a kasar nan , sakamakon rashin bin ka’idojin kasuwancin wutar lantarki da suke yi.
Duk da cewa ba a bayyana sunayen kamfanonin wutar lantarkin da abin ya shafa ba, gwamnatin ta bayyana cewa, an dora harkokin tafiyar da wutar lantarki a kasar nan, bisa doron ka’idojin samar da hasken lantarki a kasar nan.
A cewar Gwamnatin Tarayya, Dole ne kanfanoni suyi biyayya ga dokokin da gwamnati ke tafiya a kansu.
Shugaban sashin kula da harkokin na kanfanin dakon wutar lantarki na kasa Edmund Eje, ya ce a halin yanzu kanfanonin samar da wutar lantarki suna yin watsi da dokokin wanda yin hakan abun takaici ne.