Gwamnatin tarayya za ta samu kimanin naira bilyan 124 da milyan 26 a cikin shekara daya daga bangaren harajin shigo da kayayyaki cikin kasar nan, wanda aka dora bisa kaso sifili da digo 5 bisa 100 kamar yadda yake kunshe a cikin dokar tafiyar da harkokin kudi ta shekarar 2023.
Dokar kudi ta shekarar 2023 wadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a ranar 28 ga watan Mayun 2023, Ta yi tanadin cirar kaso Sifili da digoi 5 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigowa da su Najeriya daga kasashen waje.
A cewar dokar, za a dora harajin kaso Sifili da digo 5 kan kayayyakin da ake shigowa da su Najeriya daga kasashen waje.