
Gwamnatin taraiyya ta yi barazanar daukar Hayar Likitoci tare da biyansu albashi da hakkokin Likitoci masu neman kwarewa da suka shiga yajin aiki.
Ministan kwadago Chiris Ngige ne ya baiyana haka yayin wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels.
A jiya ne kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa suka fara yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyar domin ganin an biya masu bukatunsu.
Ya kuma baiyana cewar Kungiyar likitocin ta nuna rashin girmamawa ga uwar kungiyar lIkitoci ta kasa, kasancewar a yanzu haka gwamnatin taraiyya tana tattaunawa da ita a madadin kungiyar.
A wani bangaren kuma,
Gwamnatin taraiyya ta ce a yanzu haka ana tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki kan yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyar , Wanda kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta kasa ta fara a tsakar daren jiya.
Da yake amsa tambayoyin manema Labarai jiya a Abuja, Daraktan sashin kula da lafiyar al’umma na Ma’aikatar lafiya ta kasa, Dr Morenike Alex Okoh, Ya ce gwamnatin taraiyya ta damu matuka da tafiya yajin aikin.
Likitocin dai na neman a yi masu karin Albashi da kaso 200 cikin 100 daga abunda ake basu a halin yanzu.
Sai dai ministan Kwadago, Chiris Ngige ya gargadi Likitocin masu neman kwarewa kan tafiya yajin aikin da suka yi, wanda ya baiyana a matsayin haramtacce.