Ministan Birnin taraiyya Abuja, Malam Mohammed Bello Yace sama da naira Bilyan Biyu ce gwamnatin taraiyya ta amince a kashe domin siyen motoci da kayan aiki na jami’an hukumomin tsaro dake birnin taraiyya Abuja, domin inganta sha’anin tsaro a Abuja da kewayenta.
A cewarsa sabbin motoci 60 masu dauke da tsarin manhajar sadarwa ta zamani za’a siye su ne akan kudi sama da naira Milyan Dubu 1, kuma zasu dauki tsawon watanni biyu ne rak domin kawo su kasar nan.
Ministan birnin taraiyyar Abuja, ya kara da cewa, za’a siyawa hukumomin tsaro kayan aiki daban daban akan kudi naira Milyan 847.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da amincewarsa ta fitar da naira Bilyan 1 da milyan 145 domin siyawa jamhuriyar Nijar motoci kirar Toyota Land Cruiser guda 10 domin inganta sha’anin tsaro.
Wani dan jarida mai bincike David Hundeyin ne ya bayyana a shafinsa na Twitter, inda yace ya samu takarda daga ofishin kasafin kudi na kasa wadda ta nuna cewa shugaban kasar ya amince da siyan motocin.
Hundeyin ya kuma makala hoton takardar domin tabbatar da ikirarin cewa shugaban kasa ya amince da sakin kudin ga wani kamfani mai suna Kaura Motors Nigeria Limited, a ranar 28 ga Fabrairun 2022.
Da take kare sayen motocin a ranar Larabar da ta gabata, ministar kudi, Zainab Ahmed ta ce an dauki wannan mataki ne domin baiwa kasar damar kare yankunanta daga barazanar tsaro kamar yadda aka saba yi a bisa al’ada.