![](https://mmo.aiircdn.com/370/607d440da1b59.jpg)
Taron Majalisar zartaswa na kasa ya amince da bayar da wasu kwangiloli guda biyu akan kudi naira milyan dubu 24,wanda ya hada da samar da hanyoyin sadarwa na kyauta a wasu wurare guda 75 da jama’a ke amfani dasu,wanda suka hada da Filayen jiragen sama dake fadin kasar nan domin tallafawa kanana da kuma matsaikatan masana’antu.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ne ya baiyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartawa na kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadarsa dake Abuja.
ya ce wuraren sun hada da filayen jiragen sama sai Kasuwanni da manyan makarantu, inda jama'a zasu rika amfani da hanyoyin sadarwar a kyauta.
Ya kara da cewar Hukumar sadarwa ta kasa ita ce zata jagoranci gabatar da wani bangare na aikin a yayin da wani kason kuma zai kasance a karkashin kulawar ma’aikatar sadarwa da cigaban tattalin arziki na zamani ta kasa.