Gwamnatin taraiyya ta fara baza jami’an tsaronta zuwa gidajen mai domin tursasawa masu gidajen man yin amfani da POS ko kuma karbar sakon tura kudi ta banki.
Hukumar kula da harkokin albarkatun mai ta kasa ita ce ta baiwa gidajen man umarnin fara yin amfani da wannan tsari kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa da aka fitar jiya a Abuja.
To sai dai sakataren kungiyar Dillalan mai ta kasa masu zaman kansu reshen Abuja da Suleja, Mohammed Shu’aibu, Ya ce suma matsalar rashin wadatuwar kudi a hannu tana shafar kasuwancinsu, Yana mai cewar babu yadda zasu yi wasu tafiye tafiye domin yin huldodinsu da suka saba, dole sai anyi amfani da tsabar kudi a hannu.
Kazalika ya ce hanyoyin sadarwar da ake amfani dasu wajen hada-hadar kudi ta banki basu da ingancin da ake tsammanci , a saboda haka dakon samun tabbacin tura kudin da mai sayen mai zai yi a gidan mai, zai sai a samu cunkuson ababen hawa a gidajen man.