On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gwamnatin Taraiyya Tayo Odar Manyan Taransfomomi Daga Waje Domin Inganta Samar Da Wutar Lantarki

Na'urorin Transfoma

Gwamnatin taraiyya tace kason farko na Manyan Taransfomomin lantarki da shirin samar da wutar lantarki na fadar shugaban kasa yayo odarsu daga kasashen waje, zasu karaso Najeriya a cikin watan satumbar bana.

Kakakin Ministan Lantarki, Isa Sanusi ne ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar jiya a Abuja, Yace tuni aka kammala gwajin Na’urorin Transfomar da aka kera a kanfanin Siemens  dake Trento na kasar Italiya.

Ya kara da cewa tawagar  gwamnatin taraiyya wadda ta hada da injiniyoyi daga kanfanin samar da wutar lantarki na kasa, sun ganewa idonsu yadda gwajin Na’urorin Transifomar ya kasance a ranar 28 ga watan da muke ciki a kasar Italiya.