Takun sakar dake tsakanin kugiyar malaman Jami’oi ta kasa ASUU da kuma gwamnatin taraiyya ka iya kara dagulewa, biyo bayan yadda Ma’aikatar Ilimi ta kasa ta baiyana cewa yarjejeniyar dake tsakaninta da kungiyar Malaman jami’oi ta kasa, ba zata yi aiki akan jami’oin jihohi ba.
Wani kwamiti da gwamnatin taraiyya ta kafa a karkashin uban jami’ar Lokoja, Farfesa Nimi Briggs , Ya bada shawarar biyan malaman jami’oin akan karin kaso 180 bisa 100, to amma gwamnatin taraiyya tace zata yi karin kaso 100 bisa 100 ne kawai.
Kazalika Kakakin Ma’aikatar Ilimi ta kasa, Ben Goong a wata hira da aka yi dashi jiya Abuja, Ya baiyana cewa gwamnatin taraiyya ba zata tsoma bakinta kan harkokin da suka shafi tafiyar da ilimi a matakan jihohi, kasancewar yana a bangaren kebantattun abubuwa da doka ta tsara.
A martaninsa shugaban Kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodoke , Yace dole ne duk wata yarjejeniya da suka kulla tsakaninsu da gwamnatin taraiyya ta shafi jami’oin jihohin.
A yanzu dai a iya cewa a yanzu an bude wani sabon babin takaddama tsakanin gwamnatin taraiyya da kuma kungiyar ASUU.