Gwamnatin taraiyya ta samu nasarar karbo sama da naira Milyan Dubu 3 da Milyan 200 da aka sace daga kasar nan, ta hanyar yin shari’oi daban daban da aka yi a fadin duniya, daga cikin watan Maris din shekara 2021 zuwa watan Mayun 2022.
Kazaalika rahotanni sun baiyana cewa gwamnatin taraiyya ta samu zarafin tattara sama da naira bilyan 1 da milyan 82 daga kadarorin sata da aka siyar a cikin watanni 18 na farkon gwamnatin shugaban kasa Buhari.
Ministan shari’a na kasa Abaubakar malami ne ya baiyana haka yayin zantawarsa da manema Labarai na fadar shugaabn kasa.
Ya ce tuni aka yi amfani da kudaden wajen gudanar da aiyukan raya kasa.