Gwamnati taraiyya ta hannun Hukumar kula da tallace-tallace ta kasa ta Kai karar kanfanin Meta Mai Shafin Facebook da Instagram da kuma WhatsApp.
Hukumar kula da tallace -tallace ta kasa, ta Kai karar kanfanin Meta, Mai Shafin Facebook da Instagram da kuma WhatsApp da kuma kanfanin da yake masa dillanci, Mai suna AT3 resources limited, gaban wata Babbar kotun taraiyya dake Abuja.
Hukumar na neman kotun ta baiyana cigaba da wallafa talla a shafukan batare da amincewarta ba a matsayin haramtacce, Wanda Kuma ya sabawa doka a Najeriya.
Hukumar kula da tallace-tallace ta kasa, APCON ta ce cigaba da wallafa talla a shafukan na Meta batare da amincewarta ba, yasa Najeriya na asarar makudan kudin shiga.
A saboda haka ta bukaci kanfanin ya biya gwamnatin taraiyya naira bilyan 30 sakamakon keta dokar wallafa tallace-tallace da ya yi.