A yaune gwamnatin taraiyya ta gana da shugabanni da kuma Iyayen jami’oin gwamnatin taraiyya dake fadin kasar nan, a wani mataki na kokarin kawo karshen yajin aikin da kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU Ke kanyi.
A yayin ganawar, Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu ya baiyana yajin aikin sai baba ta gani da kungiyar ASUU ke kanyi, a matsayin wani abun tozarci da kuma rikitarwa.
Adamu yace akwai bukatar bangarorin biyu su cimma kwakwkwarar matsaya kan dukkakin abubuwan da aka cimma yarjejeniya a kansu a shekarar 2009, kasancewar makwanni biyu da suka gabata sun kasance mafi muni ga bangaren ilimi a kasar nan.
Ministan Ilimin ya Ambato shugaban kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, wanda ya baiyana cewa a halin yanzu kungiyar ba zata sasanta da gwamnati mai ci akan yajin aikin ba, inda ya baiyana cewa ya zama wajibi a janye matakin domin ceto fannin ilimi a kasar nan.