A yaune gwamnatin taraiyya zata fara aikin kwashe ‘Yan Najeriyar da suka makale a Khartoum babban birnin kasar Sudan, da sauran wasu birane na kasar , su kimanin dubu 5 da 500 ,biyo bayan amincewa da tsagaita wuta ta tsawon kwanaki ukku a yakin da ake gwabzawa kasar,wadda ta fara aiki a jiya.
Shugabar Hukumar kula da ‘Yan Najeriya mazauna kasashen ketare, Uwargida Abike Dabiri Erewa, ta tabbatar da cewar gwamnatin taraiyya ta fitar da naira milyan 150 domin yin hayar manyan motoci guda 40, wadanda zasu dauke ‘yan Najeriyar da suka makale a kasar domin tsallakar dasu zuwa kasar Masar.
Rahotanni sun baiyana cewar Babban bankin kasa ta hannun Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa,Ya saka kudin ta cikin wani asusun kanfanin zirga-zirgar ababen hawa da ba’a baiyana sunansa ba, domin fara kwashe mutanen daga safiyar yau.
A yanzu haka kasashen waje na amfani da tsagaita wutar da aka samu wajen kwashe ‘yan kasashensu da suka makale a kasar ta Sudan, wadda ta fada cikin rikici.