Gwamnatin taraiyya ta amince da fitar da zunzurutun kudi har naira bilyan 19 da milyan 24 domin aikin horas da masu shirin N-Power Dubu Hamsin, da kuma saka fitulu a cikin filayen jiragen saman Fatakwal da Legas da kuma Abuja.
Kazalika kudin ya kunshi biyan kudin aikin tuntuba na aikin samar da hasken lantarki mai karfin megawa 40 a jihar Gombe, ga kanfanin Dadin kowa , da kuma aikin ‘kawata shalkwatar hukumar sufurin jiragen ruwa ta kasa dake yankin Victoria Islanda a Legas.
Ministan kula da harkokin jin kai da kuma ministan sufurin jiragen sama na kasa, tare da ministan albarkatun ruwa na kasa, sune suka baiyana haka ga manema labarai, jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartawa na gaggawa da aka yi jiya.
Ministan kare afkuwar Bala’oi ta kasa, Hajiya Sadiya Faruk ta ce an fara shirin N-POWER ne tun daga shekarar 2016.