Gwamnatin Taraiyya ta bada umarnin dakatar da wasu Ma’aikata har dubu 3 batare da bata lokaci ba, bisa zarginsu da gabatar da takardar bogi na kammala karatu ga Hukumar kula da Ma’aikata ta Kasa.
Shugabar Ma’aikata ta kasa, Dr. Folasade Yemi Esan ce ta baiyana haka a ranar Laraba a Abuja, Yayin wani zauren tattaunawa da aka shirya, Domin bukin Makon Ma’aikata na bana.
Tace an gano Ma’aikatan har dubu ukku ne dauke da Takardun kammala Karatu na bogi, a sakamakon aikin tantancewar da Hukumar Ma’aikata ta kasa ke kan yi, kuma aka bada umarnin gaggauta dakatar dasu.
Tace Ma’aikatan da aka gano na zuwa ne bayan bankado karin wasu Ma’aikata Dubu 1 da 500 dauke da takardun Bogi da suke yi aiki a ma’aikatun gwamnatin taraiyya.