Hukumar Kula da sufurin jiragen sama ta kasa, Ta Dakatar da kanfanin jiragen sama na Dana Airlines har sai abunda hali yayi.
Shugaban Hukuamr Kaftin Musa Nuhu ne ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, Yace dakatarwar ta fara aiki ne daga daren jiya Laraba.
Kaftin Nuhu ya alakanta dakatarwar da aka yiwa kanfanin jiragen saman da rashin cika ka’idojin da suka shafi harkokin kudi wajen kula da lafiyar jiragensu. Ya kuma baiyana cewa tuni aka isar da sakon dakatarwar ga hukumomin kanfanonin jiragen saman.
Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta kasa, Ya kara da cewa, Daukar matakin ya biyo bayan binciken da hukumar ta gudanar kan harkokin tafiyar da kudi na kanfanin jiragen saman da aka yi a kwanan nan.