Gwamnatin taraiyya ta bukaci Kotun Koli data kori karar da aka shigar gabanta wadda ake neman a dakatar da gwamnatin taraiyya daukar matakin hana yin amfani da tsaffin kudi daga ranar 10 ga watan da muke ciki.
Idan ba’a manta ba,Babban bankin kasa ya fara saka wa’adin ranar 31 ga watan janairu a matsayin lokacin da za’a dena yin amfani da tsaffin takardun kudin kafin daga bisani ya tsawaita zuwa 10 ga watan Fabarairun da muke ciki.
A hukuncin da kotun kolin ta yanke a jiya karkashin Alkalai guda bakwai,bisa jagorancin mai shari’a John Okoro , ta dakatar da gwamnatin taraiyya daga daukar matakin hana yin amfani da tsaffin kudin , biyo bayan karar da gwamnatocin jihohin Zamfara da Kogi da kuma Kaduna suka shigar gabanta.
To sai dai a bukatar da gwamnatin taraiyya ta shigar gaban kotun,ta hannun babban lauyan gwamnatin taraiyya, Ta baiyana cewa Kotun kolin bata da hurumin sauraren shari’ar , sannan kuma masu kara basu gabatar da wasu kwararan hujjoji akan matakin da suka dauka.
Daga bisani kotun kolin ta dage zamanta zuwa ranar 15 ga watan Fabarairu da muke ciki.