Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin bude babbar gadar Naija ta biyu , domin cigaba da yin amfani da ita.
Kazalika ya shawarci masu amfani da hanya da su rika tukin cikin nutsuwa akan gadar, kamar yadda ya baiyana haka yayin bukin bude gadar da aka yi domin yin amfani da ita na tsawon wata daya, a lokacin da ake bukukuwan karshen shekara.
Da yake jawabi ta bakin ministan aiyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, Shugaban kasar ya ce makasudin gina gadar shine domin kare rayuwa da kuma rage fatara da ake fuskanta a sakamakon cunkuson ababen hawa na tsawon sa’oi da ake samu a tsohuwar gadar Naija ta farko da ake samu.