Gwamnatin tarayya ta amince da yin amfani da wani tsarin fasahar alkinta bayanai a wuri daya.
An amince da yin amfani da tsarin ne a yayin taron majalisar zartarwa na kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, farfesa Isa Pantami ya ce fasahar alkinta bayanai a wuri daya zata temaka wajen kare bayanan daga masu kutse a na’ura ko kuma yin wani abu da bai dace ba.
Pantami ya kara da cewa, majalisar zartarwar ta kasa ta umurci hukumomi da su hada kai da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa domin tabbatar da sunyi amfani da tsarin.
Ministan ya bayyana cewa fasahar Alkinta bayanai a wuri daya ta Blockchain ta dace da yin aiki bangarori da yawa kamar aikin banki da fannin tsaro da ilimi da kasuwanci da dai sauransu.