Majalisar zartarwa na kasa karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da jinginar da filayen sauka da tashin jiragen sama Nnamdi Azikwe dake Abuja da kuma filin jirgin sama Mallam Aminu Kano dake nan nan Kano.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, Wanda ya tabbatar da haka, ya ce za a jinginar da filin saman Abuja na tsawon shekaru 20, yayin da na Kano zai dauki tsawon shekaru 30 a matsayin jingina.
Hadi Sirika ya kuma baiyana cewar majalisar ta kuma amince da sauya sunan ma’aikatarsa daga ma’aikatar sufurin jiragen sama ta kasa zuwa ma’aikatar sufurin jiragen sama da kula da sararin samaniya ta kasa.
Ya ce majalisar ta kuma amince da daftarin manufofin zirga-zirgar jiragen sama na kasa da duniya ke amfani dasu a halin yanzu.