Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bai wa hukumar kula da tallace-tallace ta kasa, izinin yin sammacin kanfanin Meta, wanda shi ne mamallakin katafaren shafin sada zumunta na Facebook.
Kotun ta bayar da umarnin ne a bisa bukatar da hukumar ta shigar a gaban kotu na neman kanfanin ya biya ta Naira biliyan 30 saboda karya dokokin talla a Najeriya.
Za a tura sammacin ne kai tsaye zuwa shalkwatar kamfanin Meta dake Amurka wanda ya kasance mallakin shafukan sada zumunta na facebook da Instagram da Messenger da kuma WhatsApp.
Hukumar kula da tallace-tallace ta kasa ta baiyana cewar yadda kanfanin ke wallafa wasu tallace – a shafin nasa a nan Najeriya ba tare da samun amincewarta ba, Haramun ne, kuma ya sabawa doka.
Hukumar ta kuma yi ikirarin cewa mafi akasarin tallar da ake sakawa a shafin na Facebook a nan Najeriya ya ci karo da al'adun kasa da tanadin kundin tsarin mulki da kuma tunanin 'yan kasa.