Ministar Kudi, Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna tayi kiyasin cewa Najeriya na kashe naira Bilyan 18 da Milyan 39 a kowace rana domin biyan kudin Tallafin Mai.
Ministar ta baiyana haka ne a yayin zaman jin ba’asi da kwamitin wucin gadi na zauren majalisar wakilai ya shirya, domin jin yadda gwamnati ta biya kudaden tallafin mai daga shekarar 2017 zuwa 2021.
A cewarta an gano yawan kudaden ne a bisa bayanan lissafin da Kanfanin Mai na kasa da hukumomin da abun ya shafa suka bayar.
Ministar Kudin ta kara da cewa, Bayanai sun nuna cewa ana amfani da Lita Milyan 64 da Dubu 96 a kowace rana a kasar nan, A yayin da aka biya naira tiriliyan Daya da Bilyan 774 ga Dillalan mai masu zaman kansu a matsayin kudaden Tallafin Mai a cikin shekaru 4 da suka gabata.
A nan kuma Kwamitin wucin gadi na zauren majalisar wakilai da aka kafa domin yin bincike kan yadda gwamnatin taraiyya take biyan kudaden tallafin mai tun daga shekarar 2013 zuwa 2022,Ya tuhumi ministan kudi Kasafi da kuma tsare-tsaren cigaban kasa, Zainab Ahmed kan yadda gwamnatin taraiyya ke biyan kudaden tallafin mai.
A jawabinta, Ministar ta baiyana cewa gwamnatin taraiyya ba zata iya cigaba da biyan kudaden tallafin mai ba, kasancewar biyan kudaden ka iya sawa gwamnati ta fi yawan ciwo bashi.
Tace a yanzu gwamnatin taraiyya tayi tanadin biyan tallafin mai ne zuwa rabin shekara mai kamawa kadai, kamar yadda yake kunshe cikin daftarin kundin tsare-tsaren kasafin kudi na shekarar 2023 zuwa 2025.