On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnatin Najeriya Tana Da Tsarin Maye Gurbin Likitocin Dake Ficewa Daga Kasar - Ministan Lafiya

Gwamnatin Najeriya tace a zahiri akwai isassun likitoci a kasarnan amma gwamnatin tarayya na kokarin ganin ta maye gurbin duk wani likitan da ya bar aiki ya fice daga Najeriya.

Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire shine ya  bayyana hakan ranar talata a Abuja yayin wani taron manema labarai.

Ya kuma bayyana cewa babu wani takunkumin hana daukar likitoci aiki da sauran ma’aikatan lafiya a kasar nan.

Ministan ya bayyana cewa ma’aikatar tana aiki tare da ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati domin  yin amfani da dabarun daukar aiki ta yadda idan likita ko ma’aikacin jinya ya ajiye aiki ya tafi kasar waje za’a samu wanda zai maye gurbin aikinsa.