On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Najeriya Ta Samu Tallafin Rage Radadin Cire Tallafin Man Fetur

Gwamnatin tarayya ta ce ta samu tallafi daga bankin duniya a wani mataki na rage radadin tasirin cire tallafin man fetur.

Da take sanar da hakan da yammacin jiya Laraba bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya, ministar kudi, Zainab Ahmed ta ce tallafin ya kai dala miliyan 800.

Ta kara da cewa adadin wanda shi ne kaso na farko, an tsara rabawa gidaje miliyan 10.

Sai dai Ministar Kudin ta jaddada cewa dole ne gwamnati ta samar da karin kudade domin inganta tallafin ga ‘yan Najeriya.