On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Gwamnatin Najeriya Ta Fara Tantance Mutane Da Matsalar Tsaro Ta Shafa A Yankin Arewa Maso Yammacin Kasar

Ma’aikatar jin kai agaji da cigaban al’umma ta Tarayya ta fara tattara bayanan mutanen da rashin tsaro ya shafa a wasu kananan hukumomin jihar Katsina.

Shugabar tawagar, Hajiya Nadia Muhammed-Soso, itace ta bayyana haka ranar Alhamis a Katsina, inda ta ce manufarsu ita ce sanya wadanda abin ya shafa su kasance cikin dukkanin shirye-shiryen bunkasa rayuwar ‘yan  kasa.

Da take wayar da kan jama’a kan aikin, Muhammed-Soso wadda ke jagorantar Sashen ayyuka na musamman na ma’aikatar, ta ce wadanda abin ya shafa sun sha wahala sosai kuma suna bukatar tallafin rayuwa.

A cewarta, ma’aikatar ta fahimci babban kalubalen da wadanda ta’addancin ya shafa ke fuskanta a fadin Najeriya, kuma ta fara aikin tantancesu.